Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Frenchpeople.daily cewa, a cikin 'yan kwanakin da suka gabata mahukunta a kasar Mauritaniya sun rufe wasu cibiyoyi masu alaka da kungiyar 'yan uwa musulmi a kasar sakamakon gangami da kungiyoyin masu kishin islama suka yi a kasar.
Mahukuntan dai sun dauki wanan mataki ne kamar yadda wani bayanin ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ya yi nuni da cewa, wadannan cibiyoyin suna gudanar da ayyukansu ne karkashin inuwar wasu kungiyoyi da ba su da izinin gudanar da ayyuka na addini a kasar, kuma akwai yuwuwar su yi amfani da hakan wajen tayar da hankulan al'umma.
Al'ummar Birnin Nuwakchot babban birnin Murtanya sun gudanar da zanga-zanga don nuna bacin ransu kan yadda wasu Mutane suka shiga Massalaci a birnin Nuwaktoch sannan suka ciccira Alkur'anan dake cikin wannan Masallaci, masu zanga-zangar dai sun rufe manyan titunan birnin na Nuwakchot inda da kel jami'an 'yan sanda suka tarwatsa su sannan suka bude titunan.
Ko A ranar uku ga watan janairun da ya gabata ma, jami'an 'yan sanda na birnin Nawazibu dake arewa maso yammacin kasar sun kama Muhamad wul sheikh kan zarkinsa da cin zarfin Ma'aikin Allah tsira da amincin ... su tabbata a gareishi tare da iyalan gidan tsarkaka.inda Ma'aikata mai kula da harakar Musulinci a kasar ta bukaci Limaman juma'a na kasar baki daya da su kebe wani bangare daga cikin hudubobin nasu na juma'a don yin …. Ga masu son cin zarafin ma'akin…sanadiyar hakan dai Al'ummar kasar sun yi ta gudanar da zanga –zanga don yin ….wadai da wannan Mutune tare da duk wasu masu yunkurin yin batanci tare da cin zarafin musulinci a Duniya baki daya.
1384772