IQNA

Isra’ila Na Yin Amfani Da Halin Da Larabawa Suke Ciki Domin Rusa Qods

0:48 - March 14, 2014
Lambar Labari: 1386767
Bangaren kasa kasa, wani masanin tarihi dan yankin palastine ya bayyana cewa haramtacciyar kasar sra’ila tana yin amfani da damar da ta samu ne inda larabawa suka shagalta da kawunansu ita kuma tana shirin rusa masallacin Qods hankalinta kwance.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na palastine info cewa, Ala Abu Zahir wani masanin tarihi dan yankin palastine ya bayyana cewa haramtacciyar kasar sra’ila tana yin amfani da damar da ta samu ne a lokacin da larabawa suka shagalta da kawunansu ita kuma tana aiwatar da shirin na  rusa masallacin Qods mai alfarma.
Wasu rahotanni sun sun ce wasu Palasdinawa uku sun yi shahada sakamakon harin wuce gona da iri da jirgin saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya kai kan yankin kudancin Zirin Gaza, kakakin ma’aikatar lafiya a yankin Zirin Gaza Ashraf Al-Qidra ya bayyana cewa; Jirgin saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da babu matuki ciki ya kai hari kan wasu ‘yan gwagwarmayar Palasdinawa a garin Rafah da ke kudancin yankin Zirin Gaza a yau Talata lamarin da ya janyo shahadar Palasdinawa uku mambobi a kungiyar Jihadul-Islami tare da jikkata wasu hudu na daban.
A gefe guda kuma jirgin saman leken asirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya fado kasa a yankin garin Khun Yunus da ke kudancin Zirin Gaza, kuma majiyar rundunar sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta tabbatar da fadowar jirgin tare da dora alhakin fadowarsa kan matsalar inji. Bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas na Izzuddin Qassam ya sanar da cewar jirgin saman leken asirin ya shiga hannunsu.
1386341

Abubuwan Da Ya Shafa: palastine
captcha