Kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayyana cewa harin farko wanda yan bindiga suka kai a ranar litinin a kauyen Shawa sun kashe mutane 10 a kauyen, sannan suka kai hari na biyu a wani kauye mai suna Alagarno a ranar talata inda suka sace abicin mutanen kauyen suka kuma suka kona gidage suka kuma bude wuta kan mutanen da ke tserewa daga gidajensu.Haruna Bitrus wani dan kauyen ya fadawa AFP cewa sun kashe mutane 20 a kauyen.
Da dama daga cikin wadanda suka tsere daga wadan nan kauyuka sun nemi mafaka a garin Chibok ne.Afrika ta kudu Mazauna birnin Pretoria na kasar Afirka ta kudu sun gudanar da gangami a gaban ofishin jakadancin Najeriya domin yin kiran a saki ‘yan matan da aka yi garkuwa da su. Masu gangamin sun kirayi kungiyoyin kasa da kasa da su zage damtse domin tserato da ‘yan mata fiye da 200 da aka sace daga wata makarantar kwana ta garin Chibok a Jahar Borno. Zanga-zangar ta kasar Afrika ta kudu ta zo ne a matsayin ci gaba da kiraye-kirayen da ake yi a duniya domin matsin lamba ga kungiyoyin kasa da kasa da kuma gwamnatin Najeriya da a ceto da ‘yan matan da ake tsare da su.
A cikin watan Aprilu ne dai kungiyar nan da ake kira da Boko Haram, ta kame ‘yan mata 276 daga garin Chibok tare da cewa za su sayar da su a kasuwa.