Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, 'yan ta'addan alka'ida sun yi wa malam addinin musulunci goma sha biyu yankan rago a birnin Musil da ke arewacin kasar a ranar Alhamis da ta gabata, da suka hada har da babban limamin birnin Sheikh Muhammad Mansuri, wanda daya ne daga cikin manyan malaman Ahlu-sunnah a kasar, saboda yaki ya yi musu mubaya'a, kamar dai yadda iyalansa suka bayyana ga manema labarai.
A wani labarin kuma Kakakin rundunar sojin kasar Iraki kanar Kasim Al-ata ya fadi yau cewa, daga jiya Juma'a zuwa yau Asabar, kimanin matasa miliyan daya da rabi ne suka kai kansu a sansanonin sojin kasar, domin daukarsu aikin soji na sa-kai domin yaki da 'yan ta'addan alka'ida, ya ce yanzu haka an fara ba su horon gaggawa.
Yayin da anata bangaren kungiyar malaman Ahlu-sunnah a kasar Iraki (Jama'at Ulama Al-Iraq) ta fitar da fatawa a yau Asabar, inda ta halasta daukar makami domin yaki da 'yan alka'ida a kasar. Shugaban kungiyar Sheikh Khalid Almulla shi ne ya karanta sanarwar a yau.
1417407