
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, yanzu haka an fara gudanar da wasu shirye-shirye na shiga watan Ramadan Mai zuwa kamar dai yadda aka saba yi a kasar Zamabia tare da halartar jami’an gwamnati da kuma kungiyoyin farar hula da kuma wasi na addini.
A wani labarin kuma Uku daga cikin kungiyoyin ‘yan tawaye Abzinawa na Arewacin Mali da suka amince da yarjejeniyar tsagaita buda wuta a kwana baya sun bayana anniyar bada goyan baya ga matakin maido da zamen lafiya mai daureda a kasar Mali kamar yadda ministan harkokin wajen kasar Aljeriya ya sanar.
Kungoyiyon da suka hada da mai gogormaya kwato incin Azawad, da majalisar koli shawara al’umma Azawad da kuma kungiyar MAA ta larabawa Azawad sun kuma sanarda shiga tattaunawar nemen zamen lafiya da gwamnatain Mali. A ranar al’hamiss din maku jiyya ne dai gungun kungiyoyin ‘yan tawajen na Mali daban-daban suka hadu a birnin Alger na kasar Aljeriya a wani taro share fagen tattaunawa da hukumomin Mali tareda shiga tsakanin kasar Algeriya mai raba doguwar iyaka da kasar Mali.
Idan ana tune dama a watannin baya bangarorin biyu sunyi irin wanan ganawa a birnin Ouagadugu na kasar Burkina Faso inda suka daddale wata yarjejeniya, saida sakamakon rashin mutunta yarjejeniyar ‘yan tawayen suka sake daukan makamai.
1418065