IQNA

An Gudanar Da Wani Zaman Tattaunawa Kan Batun Boko Haram

17:01 - June 21, 2014
Lambar Labari: 1420846
Bangaren kasa, matsalar Boko Haram na daga cikin manyan matsaloli da suka zama cikin matsalolin musulmi a duniya ba a Najeriya ba kawai domin kuwa kungiyar tana cin zarafin addinin musulunci ne a baki daya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga wasu kafofin yada labarai cewa,  Ana ci gaba da taron gangami na ganin an ceto ‘yan Matan sakanderen na  garin Chibok a Najeria, a jiya Laraba Kungiyoyin fararen hula masu gwagwarmayar ganin an ‘yanto ‘yan Matan sakanderen, sama da 200 na garin chibok sun gudanar da taron gangami a birnin Abuja.
A wannan taro dai an gudanar da jawabai daban daban daga shugabanin kungiyoyin inda suka ce Gwamnatin Najeria ba ta yin abinda da ya dace na ganin ta kubuto ‘yan Matan sama da dari biyu daga hanun kungiyar boko haram
Yanzu  haka dai kimanin watanni biyu da kungiyar boko haram ta sace ‘yan Matan sakandere sama da 200 a Garin Chibok na jahar Borno Najeria amma har yanzu an kasa ceto wadannan ‘yan Mata duk da irin alkawulan da kasashen Duniya suka yi na cewa za su taimaka wajen ceto ‘yan matan cikin gaggawa
Matsalar kungiyar Boko Haram ta wurga daliban makarantun boko da suke kasar Kamaru kusa da kan iyaka da tarayyar Nigeriya cikin fargaba.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya watsa rahoton cewa: Daliban makarantun boko da malamansu da suke garin Fotokol a arewacin kasar Kamaru kusa da kan iyaka da tarayyar Nigeriya suna cikin tsananin fargaba da tsoron fuskantar farmaki daga mayakan kungiyar Boko Haram musamman inda a wasu lokuta harsasan harbe-harben bindiga suke wucewa ta kan rufin makarantunsu.
Wani dalibin makaranta ya yi furuci da cewar suna cikin hatsari da tsoro kuma hankulansu ba su kan darussan da ake koya musu, domin a kowane lokaci idonsu yana kan taga suna duban abin da zai je ya komo. Kamar yadda shi ma shugaban makarantan Fotokol high School Jean Felix Nyioto ke cewa; a kullum suna cikin shirin ko-ta kwana ne a makarantansu saboda tsaron fuskantar harin ‘yan kungiyar Boko Haram.
1418659

Abubuwan Da Ya Shafa: Boko Haram
captcha