Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, a zaman da ta gudanar a yau babbar kungiyar hadin kan mata musulmi na duniya ta yi kakakusar suk da yin Allawadai da kungiyar Boko Haram masu tsatsauran ra’ayi da ke bata sunan addinin muslunci ba a Najeriya ba kawai, har am a duniya baki daya.
A wani labarin kuma kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya watsa rahoton cewa: Daliban makarantun boko da malamansu da suke garin Fotokol a arewacin kasar Kamaru kusa da kan iyaka da tarayyar Nigeriya suna cikin tsananin fargaba da tsoron fuskantar farmaki daga mayakan kungiyar Boko Haram musamman inda a wasu lokuta harsasan harbe-harben bindiga suke wucewa ta kan rufin makarantunsu.
Wani dalibin makaranta ya yi furuci da cewar suna cikin hatsari da tsoro kuma hankulansu ba su kan darussan da ake koya musu, domin a kowane lokaci idonsu yana kan taga suna duban abin da zai je ya komo. Kamar yadda shi ma shugaban makarantan Fotokol high School Jean Felix Nyioto ke cewa; a kullum suna cikin shirin ko-ta kwana ne a makarantansu saboda tsaron fuskantar harin ‘yan kungiyar Boko Haram.
1420718