IQNA

Musulmin Afirka Ta Kudu Suna Bayar Da Buda Baki Ga Mutane

13:06 - July 03, 2014
Lambar Labari: 1425376
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a kasar Afirka suna taimaka ma sauran mutanen kasa ta hanayar basu buda bakia lokacin shan ruwa ba tare da la'akari da bambancin addinansu ba.

 

amfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na World Bulletin cewa, tun daga lokcin shigowa watan Ramadan mabiya addinin muslunci a kasar Afirka suna taimaka ma sauran mutanen kasa ta hanayar basu buda bakia  lokacin shan ruwa ba tare da la'akari da bambancin addinansu ba da suke bi a kasar.

A wani labarin kuma ma’aikata na babban Kungiyar ma’aikata a kasar Africa ta kudu sun fara yajin aiki na sai baba ta gani a jiya Talata a duk fadin kasar, ma’aikatan sun fara yajin aikin ne  bayan da tattaunawa tsakanin shuwagabannin kungiyar da kuma ministan masan’antun kasar Mildred Oliphant ya kasa dakatar da yajin aikin.
Ma’aikatan dai suna bukatar karin kashi goma na albashinsu da kuma allawus na gidajen zaman, masana sun bayyana cewa yajin aikin ya dakatar da ayyuka a ma’aikatu kimani dubu 10 a duk fadin kasar, kuma zai iya gurgunta tattalin arzikin kasar so sai idan ya yi tsawo.
Yajin aikin na babban Kungiyar ma’akatan kasar Africa ta Kudu ya zo ne jim kadan bayan da kungiyar ma’aikatan Ma’adinai suka kawo karshen nasu yajin aikin wanda ya kai tsawon watanni kima biyar a cikin yan kwanakin da suka gabata. Yajin aiki na ma’aikatan ma’adinai na kasar dais hi ne yajin aikin mafi tsawo wanda ma’aiakata suka taba yi a tsawon tarihin kasar.
1424632

Abubuwan Da Ya Shafa: afrika
captcha