IQNA

An Shiga Rana Ta Shida A Gasar Karatun Kur'ani Ta Dubai

10:07 - July 13, 2014
Lambar Labari: 1428910
Bangaren kasa da kasa, gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki da ake gabatarwa a cikin watan Ramadan mai alfarma tare da halartar makaranta a wannan karon ma kimanin mutane tamnin da bakwai ne suka halarci gasar wadda take gudana yanzu haka.

  Kamfanin dilalncin labarana kur'ani na Iqna ya habarta cewa, makaranta 7 ne suka kara da juna, bayanin ya kara da cewa an nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Darul khalij cewa, idan Allah ya kai mu gobe ne za a bude babbar gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasar hadaddiyar daular larabawa da aka saba gudanarwa a kowace shekara tare da halartar makaranta daga kasashen duniya musamman ma kasashen musulmi daga cikinsu. Wannan gasar dai it ace ta goma sha biyu da za a gudanar a kasar a birnin, tare da halartar makaranta da mahartdata su 87, daga kasashe da dama wadanda za su kara da juna, daga karshe kuma za a fitar da mutane sha shida da za a baiwa matsayi na farko da na biyu da uku a dukkanin bangarorin da za a gudanar da gasar ta kur'ani mai tsarki. Daga bangarorin gudanar da gasar dai sun hada da karatun kur’ani mai tsarki a bangaren tartili da kuma tangimi, sai kuma bangaren hardar kur’ani, da hakan ya hada da bangaren hardar kurani baki daya, sai kuma bangaren masu hardar juzui, kama daga kasa zuwa sama, kamar dai yadda aka saba gudanar da wannan gasa a kowace shekara a cikin watan Ramadan.

1428514

Abubuwan Da Ya Shafa: gasa
captcha