Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, kakakin ma'aikatar kiwon lafiya a yankin gaza Ashraf Qudrah ne ya sanar da hakan a daren jiya, inda ya ce adadin yana karuwa bisa la'akari da tsananta hare-haren na Isra'ila a kan al'ummar Gaza, da kuma yadda wasu daruruwan mutane suke cikin mawuyacin hali, sakamakon raunukan da suka samu.
A nata bangaren gwamnatin kasar Masar ta gabatar da wata shawara da ke neman dakatar da bude wuta tsakanin Isra'ila da kuma kungiyoyin Palastinawa 'yan gwagwarmaya da ke yankin Zirin Gaza a yau Talata.
Firayi ministan Haramtacciyar kasar Isra'ila Benyamin Natenyahu ya yi lale marhabin da hakan, kamar yadda shi ma shugaban kasar Amurka ya nuna gamsuwarsa da wannan shawara, yayin Hamas ta ce ba za ta amince da dakatar da bude wuta ba har sai Isra'ila ta daina kai hare-hare kan al'ummar Gaza.
Kasashen larabawa dai sun kasa tabuka komai a kisan gillar da haramtacciyar kasar Isra'ila take yi wa fararen hula a yankin na Gaza, wanda hakan ya kara fito da matsayinsu a fili na zama 'yan Koran yahudawa.
1428938