Mai aiko ma tashar talabijin alam rahotanni daga yankin Gaza ya sheda cewa, jiragen yakin na Isra'ila sun kaddamar da harin ne a kan wannan asibiti saboda gudunmawar da take bayarwa wajen yin magani ga wadanda suka jikkata sakamakon hare-haren na Isra'ila, inda ta biyo su a wurin ta karasa wasu daga cikinsu da suka kai mutum 30, kamar yadda kuma wasu hare-haren makamantan wannan a kan sansanin majalisar dinkin duniya suka yi sanadiyyar yin shahadar mutane 16.
Majiyoyin asibiti sun tababtar da cewa adadin Palastinawa da suka yi shahada ya zuwa yau a cikin kwanaki 16 ya kai 804, yayin da wasu fiye da dubu biyar suka samu raunuka, wasu daga cikinsu na a halin rai kwakwai mutu kwakwai.
Gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila da kuma kungiyar Hamas a yankin Gaza sun amince da tsagaita bude wuta na sa’oee 12 a yau asabar don bada dama ga ayyukan agaji da kuma dan sararawa ga wadanda suke takure.
Tsagaita bude wutan zau soma ne daga karfe 8 na safen agogon yankin ma’aikatar cikin gida a yankin gaza ta gargadi Palasdinawa a yankin da su guji zuwa sansanonin dakarunsu don gujewa tashin boma bomai ko kuwa zuwa kusa da ruzazzun gidaje don kaucewa rubtawarsu.
Sekatarin harkokin wajen kasar Amurca wanda yake ta zagayawa a yankin don samarda yerjejeniyar tsagaita bude wuta ya ce har yanzun babu wata alaman nasara a kokarin nasa.
Ya zuwa safiyar yau Asabar dai adadin shahidan Palasdinawa a yankin na Gaza ya kai mutane fiye da 800 wasu kungiyoyin kare hakkin bil’adam sun bayyana cewa kashi tamanin fararen hula ne sannan darida casain daga cikinsu yara kanana.
Majiyoyin asibiti a Zirin gaza sun ce jiragen yakin yahudawan sun kai hare-haren ne a kan gidajen mutane fararen hula da ke yankin Khanyunus da ke cikin Zirin Gaza da safiyar yau Asabar, inda suka kashe fararen hula ashirin da suka hada da mata da kananan yara.
Majiyoyin suka kara da cewa ya zuwa yanzu adadin wadanda suka yi shahada a yankin Zirin Gaza a cikin kwanaki 17 da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kwashe tana kai hare-hare babu kakkautawa kan al'ummar yankin, ya kai mutane dari takawai yayin da wasu dubbai suka samu raunuka.