Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Almisriyun cewa, har yanzu wasu daga mahukunta a kasar Masar suna nuna rashin amincewarsu da koyar da wasu daga cikin darussa da suka shafi mu'ujizar kur'ani a kasar wadad day ace daga cikin manyan kasashen musulmi.
A wani labarin na daban an kai hari akan bututun iskar gas a yankin sina da ke kasar Masar. Rahotannin da su ke fitowa daga kasar ta Masar sun ce da safiyar yau alhamis ne wasu mutane da ba a kai ga tantance su ba, su ka kai hari akan bututun da ke daukar Iskar gaza a garin al-arish da ke arewa da yankin sinaa. Shedun ganin ido sun ce harin ya yi sanadin fashewar bututun sannan kuma da tashin gobara.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake kai wa bututun iskar as a da ke isa h.k. ra’ila da kuma Jordan, a yankin na Sinaa hari a kasar Masar. Yankin na inaa na cike da kungiyoyin da su ke dauke da makamai wadanda su ke fada da gwamnatin kasar ta Masar.