IQNA

Babban Malamin Masar Ya Bayar Da Kyautar Kur'ani Ga Shugaban EU

21:45 - September 11, 2014
Lambar Labari: 1449079
Bangaren kasa da kasa, babban malami mai bayar da fatawa v akasar Masar Shauki Allam ya bayar da kyautar kwafin kur'ani mai tsarki da aka tarjama zuwa ga shugaban kungiyar tarayyar turai.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Ahram ta kasar Masar cewa, a wata tafiya da ya yi zuwa nahiyar turai babban malamin kasar Masar Sheikh Shauki Allam ya bayar da kyautar kwafin kur'ani mai tsarki da aka tarjama zuwa ga shugaban kungiyar tarayyar turai da nufin kara fito da hakikanin ma'anar musulunci ga al'ummar wanann nahiya.

A yayin ganawar shehin malamin ya bayyana cewa ko shakka babu wasu suna yin amfani da sunan addinin addinin muslunci wajen tafka ta'asa, wanda kuma hakan ya yi mummunan tasiri musamman ma  acikin a cikin zukatan l'ummomin nahiyar turai, wanda hakan ya sanya ala tilas malaman addinin muslunci su mike domin fito da hakikanin fuska da koyar ta addinin muslunci.

Ya kara da cewa akwai wadanmda suke da'awar jihadi da kuma kafa abin da suka kira daular muslunci suna aikata ayyuka na ta'addanci duk da sunan addinin musulunci, ya ce wannan ba shi a cikin muslunci kuma dole ne al'ummomin nahiyar turai su bude idanunsu domin sanin muslunci na hakika.

Daga karshe malamin ya mika kwafin kur'ani da aka tarjama a cikin harsuna biyu, wato harsunan turancin ingilishi da kuma faransanci ga shugaban kwamitin zartarwa na kunmgiyar tarayyar turai.

1448750

Abubuwan Da Ya Shafa: Kuran
captcha