Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cdwa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Halal Fucus cewa, babban daraktan bangaren kula da harkokin kasuw3anci da tattalin arziki na kungiyar kasashen musulmi Dr. Raja Muhammad Abdullah yana cewa akwai hasashen cewa daga nan zuwa shekara ta 2050 da dama daga cikin al’ummomin kasashen nahiyar turai za su shiga addinin muslunci da gaske.
Jami’in y ace wannan sakamako ne na binciken da masana suka gudanar dangane da yadda mutanen wadannan kasashen suke yin bincike kan addini kuma suke karbarsa idan sun fahimci yadda yake, domin kuwa addinin musulunci yana kira ne zuwa ga zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai da kuma al’ummomi da suke biyayya ga wadannan addinai, sabanin abin da suke tunani.
Y ace ko shakka babu wannan zai kara karfafa gwiwarsu wajen shiga cikin harkokin kasuwanci tare da kasashen muuslmi da kuma kamfanoninsu, a lokacin za su kara gane cewa muuslmi da addinin muslunci suna da tsari a cikin addininsu kuma sabanin abin da duk suke zato dangane da su, kuma ko shakka bau hakan zai babbar tasiri da zai karkatar da zukansu zuwa musulunci.
1449736