IQNA

Samun Makarantun Kur’ani Tare Da Masallatai A Ethiopia Na Ci Gaban Musulunci

22:52 - October 01, 2014
Lambar Labari: 1456411
Bangaren kasa da kasa, bunkasar masallatai da kuma gina makarantu da ake yi a gefen masallatai domin karantar da kur’ani mai tsarkia a cikin biranan kasar Ethiopia wata alama ce ta gagarumin ci gaban da muslunci ke samu a kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarat cewa, banagaren yada labaransa na aksashen ketare daga nahiyar Afirka ya bayar da rahoton cewa a wani bayani da ya yi wa Iqna, shugaban karamin ofishin jakadancin Iran a kasar Ethiopia Sayyid Kazem Niya ya bayyana cewa gina masallatai da kuma gina makarantu da ake yi a gefen masallatai  domin karantar da kur’ani mai tsarkia a cikin biranan kasar Ethiopia wata babbar alama ce kan gagarumin ci gaban da muslunci ke samu.

Jami’in ya ci gaba da cewa a cikin tarihin muslunci al’ummar kasar Habasha sun kasance a sahun gaba wajen buga kyakyawan misali na kyawawan dabiunsu da kuma karbar baki tare da mtunta su, kamar yadda tarihin musulunci ma ya tabbatar da hakan, inda musulmin farko da makka ta gagare su zama saboda cutarwar mushrikai, manzon Allah da kansa ne ya ba su shawara da su hijira zuwa Habasha wato Ethiopia, domina  can akwai sarki wand aba a zalunta kowa a wajensa.

Wannan sheda da manzon Allah ya bayar dangane da al’ummar Habsha ta bayyana a aikace daga abin da wannan sarki ya aikata, kuma a halin yanzu muslunci yana ci gaba da samun karbuwa daga al’ummar kasar wadanda akasarinsu mabiya addinin kirista ne, kamar yadda suke tun a cikin tarihinsu.

1455560

Abubuwan Da Ya Shafa: habasha
captcha