Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, ana shirin gudanar da wani zaman taro a kasar Masar dangane da irin kalu bale da addinin muslunci yake fuskanta da kuma yadda ake kallonsa daga waje da kuma yadda masu tunani suke tunani a kansa da kuma yin hukunci a kansa.
Abbas Shouman mataimakin shugaban cibiyar Azahar ya bayyana cewa, wannan taro yana da matukar muhimmanci, domin kuwa a za a I amfani da wannan damar domin muhimamn batutuwa da suka hada da batun hakkokin marassa rinjaye, wanda hakan ya hada da musulmi a wasu kasashen, kamar yadda kuma ya hada da wasu mabiya addinai a cikin kasashen musulmi, da yadda ya kamata kowa ya samu hakkinsa ba tare da wata tawaya ba.
A bangare guda ya ce taron zai dubi a kan batun ta'addanci da tsatsauran da woce gonad a irin da ake samu a cikin musulmi, inda wasu sukan fake da sunan addinin musulunci suna gudanar da ayyuka na ta'addanci da bakanta sunan addinin, duk kuwa da cewa akasarin musulmin duniya bas u amince da wannan mummunan tunani da akida ba ta ta'addanci da sunan a ddinin muslunci.
A taron za a gayyaci wasu bangarori da suke da makamloli da za su gabatar domin kara samun fahimtar juna da kuma matsayin muslunci kan lamurran ada aka ambata danagne da manufar gudanar da taron.