IQNA

Yan Takfiriyyah Suna Amfanin Da Sunan Addini Domin Burinsu

23:20 - October 26, 2014
Lambar Labari: 1464220
Bangaren kasa da kasa, babban mai bayar da fatawa na kasar Lebanon ya bayyana cewa masu dauke da mummunar akidar nan ta kafirta musulmi da suke aikata ta'addanci da sunan addini, suna yin hakan ne domin cimma burinsu kawai.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, sheikh Abdullatif Daryan babban mai bayar da fatawa na Ahlu sunna na kasar Lebanon ya bayyana cewa masu dauke da mummunar akidar nan ta kafirta musulmi da suke aikata ta'addanci da sunan addinin musuluncikuma suna yin hakan ne domin cimma burinsu da kuma bata sunan wannan addini mai tsarki.

An bayyana cewa manufar masu akidar kafirta mutane da ake kira “Takfiriyya’ shi ne bakanta sunan addinin Musulunci a duniya. A nasa bangaren wani dan Majalisar shawarar Musulunci ya bayyana cewa; Masu akidar takfiriyya suna aiki ne domin bata sunan addinin Musulunci da kuma rusa tafarkin gwagwarmaya.

Ya ci gaba da cewa; A cikin watannin bayan nan ayyukan da masu akidar takfiriyyah su ka yi ya tabbatar da cewa ba su da wata alaka da addinin Musulunci, kuma kiyayyarsu da sukkanin musulmi ne shi’a da sunna. Dan majalisar ya kuma kirayi dukkanin al’ummar musulmi da su hada kawukansu a wuri guda domin kalubalantar  makiyan addinin Musulunci.

1463621

Abubuwan Da Ya Shafa: lebanon
captcha