Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar yaum Sabi ta kasar mara cewa, Sheikh Abdolaziz Al-sheikh babban mai bayar da fatawa a kasar Saudiyya bayan kwashe tsawon shekaru yana kiran 'yan ina da kisa na kungiyoyin daesh ISIS da Nusra masu jihadi a yau ya fito ya ambace su da 'yan ta'adda batattu.
Wani rahoto kuma dangane da batun 'yan ta'addan rundunar sojin kasar Iraki ta sanar da hallaka mutum na biyu a cikin kungiyar 'yan ta'adan Daesh ko kuma ISIS da ake kira Salah Al-zub'I, wanda ya shahara da rashin imani wajen yanka dan adam da sunan jihadi a tafarkin Allah.
Babban kwamnadan rundunar sojin Iraki da ke jagorantar farmaki kan mayakan na 'yan ta'addan ISIS masu da'awar jihadi a Iraki da Syria Brig. Janar Faisal Alsobi ya fadi yau cewa, dakarunsa sun artabu mai tsanani a yau tsakaninsu da 'yan ta'addan ISIS a kusa da garin Falluja da ke cikin gundumar Anbar, inda suka samu nasarar hallaka adadi mai yawa na 'yan ta'addan, daga cikinsu hard a mataimakin shugaban kungiyar Abubakar Bagdadi.
Babban jami'in sojin ya ce tun bayan kashe Salah Alzobi a yau, yan ta'addan ISIS sun shiga cikin rudani da firgici, inda wasu daga cikinsu suka mika kansu da makaman da ke hannunsu ga jami'an tsaro, ya kara da cewa wannan na daya daga cikin manyan nasarorin da dakarun na Iraki suka samu tun bayan fara kaddamar da hare-hare a kan 'yan ta'addan.