IQNA

Shiru Da Kasashen Musulmi Suke Yi Shi Ne Ke Karfafa Gwiwar Isra’ila Kan Ta’addanci

16:15 - November 12, 2014
Lambar Labari: 1472738
Bangaren kasa da kasa, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa irin matakin da kasashen musulmi suka dauka na nuna halin ko in kulak an abin da ke faruwa a palastinu shi ne ke karfafa gwiwar ta’addancin Isra’ila.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-alam cewa mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa irin matakin da kasashen musulmi suka dauka na nuna halin ko in kulak an abin da ke faruwa a palastinu shi ne ke karfafa gwiwar ta’addancin Isra’ila kan ta’addanci da take aikatawa kan al’ummar Palastinu.
Wasu bayanai sun ce yahudawa sahyuniya 'yan kaka gida masu tsatsauran ra'ayi dauke da bindigogi sun banka ma wani masallaci wuta a kauyen Al-mugir da ke yankin gabar yamma da kogin Jordan, inda suka kone shi kurmus.
Jami'an gwamnatin kwarya-kwarya cin gishin kai ta Palastinawa sun ce yahudawan sun killace masallacin ne suna dauke da makamai, ta yadda Palastinawan da ke wurin ba za su iya tunkararsu ba, inda suka banka wuta kan masallacin tare da cikakkiyar masaniya daga jami'an tsaron Isra'ila, wanda kuma ba shi ne karon farko da suke yin hakan ba a wannan kauye, inda a cikin  dubu biyu da sha biyu sun kone wani masallaci a wurin.
A cikin 'yan kwanakin nan dai yahudawan sahyuniya suna kai farmaki kan yankunan palastinawa da ke gabacin birnin Qods da kuma gabar yamma da kogin Jordan, inda suke kone masallatai da kuma makarantu gami da kaddarorin palastinawa, kamar yadda jami'an tsaron yahudawan na Isra'ila suke bi gida-gida suna kame matasa.
1472189

Abubuwan Da Ya Shafa: Abdollahiyan
captcha