Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Daily Star cewa, Sheikh Abdollatif Daryan babban malamin mabya ahlu sunnah a kasar Lebanon mai bayar da fatawa ya jaddada wajabcin da ke akwai kan al’ummar musulmi da su mayar da hankali kan batutuwa na hadin kai a tsakanin dukkanin mabiya addinin muslunci da dukkanin mazhabobinsu.
Shehin malamain ya ci gaba da cewa bisa la’akari da yanayin da ake cikia halin yanzu akwai bukatar fadaka fiye da kowane lokaci da ya gabata idan aka yi la’akari da irin makarkashiya da makircin da ake shirya ma musulmi domin ganin an tarwatsa su.
Ya kara da cewa masu dauke da mummunar akidar nan ta kafirta musulmi da suke aikata ta'addanci da sunan addinin musuluncikuma suna yin hakan ne domin cimma burinsu da kuma bata sunan wannan addini mai tsarki.
A cikin watannin bayan nan ayyukan da masu akidar takfiriyyah su ka yi ya tabbatar da cewa ba su da wata alaka da addinin Musulunci, kuma kiyayyarsu da sukkanin musulmi ne shi’a da sunna. dan majalisar ya kuma kirayi dukkanin al’ummar musulmi da su hada kawukansu a wuri guda domin kalubalantar makiyan addinin Musulunci.
1472558