IQNA

Kaddamar da wasikar Imam Musa Kazim (AS) a shafin koyarwa ta musulunci a washigton

14:14 - February 07, 2009
Lambar Labari: 1741276
Cibiyar Al'adu da koyarwa ta musulunci a Washington ta hanyar sadarwa ta kaddamar da Wasikar Wailat ta Imam Musa Kazim (AS) a shafinta .
Cibiyar koyar da Alkur'ani a nan Irna Iqna ta watsa rahoton cewa;gajeran bayani kan rayuwar Imam Kazim (AS) ,Ruwayoyi takwas da suka shafi mu'ujizar Imam Musa Kazim (AS),Fuska biyu ta bani Abass , Imam Kazim (AS) a karkashin inuwar Alkur'ani,Imam na Bagwai da tattalin arziki duka na daga cikin abubuwan daban-daban da wannan nwasika ta musamman ta kumsa.
Hanyoyin tarbiyar Imam Kazim (AS),daci da shahadar Imam Kazim(AS) suna daga cikin Karin abubuwan da za mu gani da karantawa a cikin wannan Wasika ta musamman. Sunan limaminmu na Bakwai ,Musa da ake yi masa lakabi da Kazim (AS) kuma ana yi masa kuniya da Abul Hasan da Abu Ibrahim. Yan shi'a da masoyansa na yi masa lakabi da kofar bukatu.Imam Musa Kazim (AS) an haife shi ne a ranar Lahadi bakwai ga watan Safar na shekara ta 128 Hijira Kamariya a garin Abwa'a. Lokacin imamancin limami na bakwai Hadrat Musa bin Ja'afar (AS) yayi daidai da shekaru na karshe na khalifancin Manzur Abasi kuma farkon khalifancin Hadi kuma shekaru 13 na khalifancin Harun kuma wannan lokaci ne yafi tsanani a rayuwar wannan bawon Allah.

Imam Musa Kazim (AS) yan dan kimanin shekaru 21 karkashin wasicin ma'aifinsa ya karbi yagorancin al'umma karkashin umarnin Allah kuma ya yi kusan shekaru 35 yana limamanci da hakan ya nuna shi ne yafi sauran limamai bayan imam Zaman (AJ) tsawon shekaru na limamanci.Imam Musa Kazim (AS) ya himmatu wajen tarbiyartar da al'ummar musulmi da fadakar da al'umma muhimmanci aurar da yayansu ga yaya salihai domin samun zurriya ta gari.


359290
captcha