IQNA

Le monde : hukumomin kasa da kasa sun bar Gaza cikin halin da ta sami kanta

15:14 - February 07, 2009
Lambar Labari: 1741295
Bangaren daga hulda ta kasa da kasa: Jaridar Le Monde da ke fitowa daga kasar Faransa a yau 16 ga watan Bahman a cikin wata makala mai suna " hukumomin kasa da kasa sun bar Gaza cikin halin da ta sami kanta" inda ta yi bincike da nazari kan gudummuwar da hukumomi na kasa da kasa suka kai wa Gaza.
Cibiyar koyar da Alkur'ani ta Iran Iqna bayan ta nakalto daga majiyar Aljazira net ta watsa labarin cewa: a cikin wannan makala Saruj Halimi mai nazari dan asalin kasar Labanon ya rubuta cewa: hukumomi na kasa da kasa bas u nuna da gasket suke ban a hukumta shugabanni da komandodin sojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila da suka tabka leifukan yaki a harin da suka kai wa Gaza.Wannan mai nazari dan Faransa mai shekaru 61 a cikin wannan makala ya jaddada cewa: sojin Isra'ila sun ruguza da dama daga cikin cibiyoyi da gidajen da aka gina su da dukiyoyin kasashen kungiyar tarayyar Turai kuma adaidai wannan lokaci kungiyar tarayyar Turai bat a maida martini ko sau daya ba.

Saruj Halimi a cikin makalar ya yi tunatarwa da cewa : majalisar dokoki ta Amerika ta kare ta'addancin Isra'ila ka Gaza ta hanyar fitar da kudurin cewa Isra'ila tana kare kanta net a hanyar kisan gilla da gare dangin fararen hula a Gaza. Wannan lamari na nuni da rashin adalcin Yammaci musamman Amerika mai kare manufar Haramtacciyar kasar Isra'ila ta kawar da Hamas.
359373
captcha