Hujjatul Islam Da MUsulmi Ali Akbar Rishad mamba komitin koli na juyi musulunci da kuma al'adu har ila yau shugaban hukumar ci gaban al'adu da tunani irin namusulunci da kuma Zahra Dabib Zade Nuri mai bawa shugaban kasa shawara kuma shugabar cibiyar kula da sha'anin Mata da Iyalai a ofishin shugaban kasa suna daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi a wajen bude taron.
Har ila yau domin muhimmancin wannan taro da abubuwan da aka tattauna a gurin taron an kafa komitoci bakwai da za su lura da kare hakkin iyali da kuma bada amsa ga wasu makaloli goma da aka kaddamar da suka shafi lamurra na cikin gida da na kasa. Abin tuni wannan taro da aka bude a ranar 19 ga watan Bahman zai kwashe kwanaki uku ana gudanar da shi.
360624