Bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Islamonline cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna ta watsa rahoton cewa: Ikbal Batol shugaban majalisar musulmin Ostriya a ci gaba da nuna adawa da hare-haren da HKI ta kaiwa Yakin Zirin Gaza na rashin tausayi da dabbanci ya bayyana cewa: akwai cikakkun dalilai masu yawa da gamsarwa da suka tabbatar rashin imani da tausayi da dabbancin HKI kan al'ummar Palasdinu a Gaza. Ya kara da cewa kisan gilla da kiyashi da jikkata dubbai Mata da kananan yara da tsaffi na nuni da Holokos na hakika da babu wani holokos da yafi wannan HKI ta aikata a yankin Gaza.
361163