IQNA

An fara gudanar da zaman tattaunawa tsakanin kasashen musulmi da kuma Amurka a birnin Doha na kasar Qatar a karo na shida.

14:10 - February 15, 2009
Lambar Labari: 1744493
Kamfanin dillancin labaran alkur'ani na Ikna ya nakalto daga jaridar (Peninsula) cewa za a kwashe kwanaki uku ne ana gudanar da zaman, kuma masana kan harokokin siyasa da tattalin arziki da shugabannin kungiyoyin farar hula ne ne suke halartar zaman, inda ake tattauna muhimman batutuwa da ke jawo takun saka da kallon hadarin kaji tsakanin duniyar musulmi da kuma Amurka.
A gefen zaman kuma an nuna wasu ayyuka da suka shafi fagage daban-daban na ilimi.

Haka nan kuma a karon farko a wannan zaman an baiwa batun matasa muhimmanci matuka, bisa la'akari da cewa matasa 'yan kasa da shekaru 30 su ne kashi 60% cikin dari a duniyar musulmi.

A yayin zaman kuma za a tattauna wasu batutuwa da suka shafi al'adun musulmi, rikin larabawa da Haramtacciyar Kasar Isra'ila, matsalolin tattalin arziki na duniya, batun makamashi a cikin karni na 21, yaduwar ilimi, tasirin zuwan Obama a fadar white house ga duniyar musulmi, da ma wasu batutuwan da za a yi dubi a kansu a yayin zaman.

363723
captcha