Kamfanin dillancin labaran alkur'ani na na Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Morocow (MAP) cewa wannan taron kungiyar malaman addinin Musulunci ta kasar ce ta shirya shi, kuma ana gudanar da taron ne a lokacin da ake gudanar da kasuwar baje koli ta littafan addini a birnin na Kazablanka a karo na 15.
Nuruddini Miladi shugaban cibiyar bincike kan kan adabin larabci da addini Musulunci a jami'ar Hameton ta kasar Birtaniya da ma wasu masana daga kasashe daban-daban na halartar wannan taro.
Daya daga cikin manufofin gudanar da taron ita ce kara fito da hakikanin surar Musulunci ta hanyar kafofin yada labarai.
Tun bayan kai harin 11 ga watan Satumba a shekara ta 2001, wasu 'yan tsiraru a kasashen turai suke ta yin amfani da wannan damar domin bata fuskar addinin Musulunci, tare da kokrin danganta addinin Musulunci da ayyukan ta'addanci, kafofin yada labaran Jamus na kan gaba wajen kokarin bata sunan addinin Musulunci a duniya.
Kungiyar Malaman addini ta kasar Morocow tana yin amfani da irin wannan damar wajen kara zaburar da musulmi da su yi amfani da kafofin yada labarai, wajen bayyana wa duniya hakikanin koyarwa ta addinin Musulunci, musamman ma ga duniyar yammcin turai.
363820