IQNA

Za a gudanar da taron shugabannin majalisun dokoki na kasashen musulmi kan batun Palastinu

16:30 - February 16, 2009
Lambar Labari: 1744719
Bangaren siyasa: Shugaban majalisun dokoki na kasashen musulmi ya bayyana cewa nan bad a jimawa ba za su gudanar da wani taro a Tehran, domin tattauna batutuwa da suka shafi Palastinu.
Cibiyar kula harkokin alkur'ani ta Iran Ikna, ta nakalto daga bangaren yada labarai na majalisar shawara ta kasar Iran cewa; shugaban malalisar kuma shugaban majalisun dokoki na kasashen musulmi Ali Larijani, ya bayyana cewa batun palastinu shi ne batu mafi mushimmanci a halin yanzu day a kamata majalisun dokoki na kasashen musulmi su yi dubi kansa, a kan haka ya tuntubi wasu daga shugabannin majalisun dokokin da ke cikin wannan kungiya, daga cikin wadanda ya tuntuba kuwa har da shugaban majalisar dokokin Nigeria, da kuma shugaban majalisar dokokin Sudan, kan batun gudanar da taro a birnin Tehran nan ba da jimawa ba kan batun na Palastinu.

364371
captcha