Bangaren kasa da kasa: Kisan kiyan da Haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi kan al'ummar gaza a cikin 'yan lokutannan shi ne mafi muni a cikin shekaru 60 da suka gabata, wanda ya yi sanadiyar yin shahadar mutane sama 1300.
Cibiyar kula da harkokin alkur'ani ta Iran ikna ta nakalto daga kafar yada labarai ta Aljazeera net cewa; a wani taro da ak bude a birnin Ribat na kasar Morocow kan hare-haren ta'addanci da Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta kai kan al'ummar Gaza, mahalarta taron sun tabbatar da cewa tun daga shekara ta 1948 da yahudawa ke yi kisan gilla kan Palastinawa, wannan shi ne mafi muni daga cikin irin wannan kisan kiyashi da yahudawan ke yi kan al'ummar palastinu.
364403