IQNA

'Yan Majalisar Dokokin Birtaniya Na Kan Hanyar Isa Gaza Domin Kai Agaji Ga Al'ummar Yankin

22:48 - February 18, 2009
Lambar Labari: 1745861
Bangaren kasa da kasa: 'Yan majalisar dokokin Birtaniya 10 na kan hanyar isa zirin Gaza, domin kai taimako ga al'ummar yankin da Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta kaiwa hare-haren ta'addanci a makonnin baya.
Cibiyar kula da harkokin alkur'ani ta Ikna, ta nakalto daga kamfanin dillancin labaran Sana cewa; a cikin ziyarar ta 'yan majalisar Birtaniya za su duba irin barnar da sojin yahudawa suka yi kan al'ummar Gaza, domin ganewa da kuma tabbatar wa duniya hujja kan ayyukan ta'addancin yahudawan sahyuniya, da kuma cancantar a gurfanar da su gaban kotun manyan laifuka ta duniya, 'yan majalisar ta Birtaniya na dauke da taimakon kayayyakin abinci, motocin daukar kaya da na dauakar marassa lafiya, da wasu kayayyakin bukatar rayuwa, domin mika su ga mabukata a Gaza.

365265

captcha