IQNA

Obama Ya fahimci Cewa: Riko Da Hakkokin Musulmi Shi Ne Zai Kawo Canji A Duniya

14:07 - February 19, 2009
Lambar Labari: 1746032
Bangaren Siyasa: Mamba a komitin zartarwa a majalisa ya bayyana cewa; Obama dole ya san cewa: kawo canji a siyasar duniya dole ya samo asali daga kare hakkokin musulmi musamman musulmin Iraki,Afganistan,Labanon da Palasdinu. A yan shekarun baya-bayan nan Gwamnatin Bush ya aiwatar siyasar kuskurai da tamka leifuka.
Cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa: Hamid Rida haji Babayi mamba a komitin zartarwa na majalisar dokokin Iran a jiya laraba ne ya yi nuni da zabar Obama a matsayin shugaban kasar Amerika da cewa: daga lokacin da aka zabe shi da rantsar da shi a kan wannan mukami ake has ashen zai kawo canji da sauyi a a duniya don haka Obama ya kwan da sanin cewa: babu wani canji matukar bai safi lamarin musulmi ba a duniya tare da kare masu hakkokinsu da ake dannewa.kuma dole ya kasance tattaunawa da Iran ba tare da wani shari ko kace nace ba matukar yana son abin ya yi armashi da kima a idon duniya da kawo canji ba rayawa ba kamar yadda gwamnatocin da suka gabace shi suka saba yi a siyasarsu ta kasa da kasa.

366074
captcha