Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Al-ilm) ta kasar Morocow cewa; masu tsattsuran ra'ayin 'yan mazan jiyan na kasar Spain sun bayana hakan ne bayan da ma'aikatar kula da harkokin iliki ta kasar ta sanar cewa za a shigar da wani darasi a cikin darussan da ake koyar da yara a makarntun kasar da ke koyar da tarbiya a koyarwa irin ta addinin musulunci, wanda ma'aikatar kula harkokin ilimi ta kasar Spain din ta ce ko shakka babu zai taimaka wajen koyar da kyakkyawar tarbiya tsakanin matasan kasar, amma masu ra'ayin 'yan mazan jiya na kasar sun ce hakan ba za ta sabu ba, duk da cewa da dama daga cikin al'ummomin kasar sun yi na'am da wannan tsari.
367262