Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; bisa ga bincike da masana kan harkokin lafiya suka gudanar, sauraren karatun suratul Fatiha da Tauhid, na kawo natsuwa a cikin zuciyar dan adam da kuma kwakwalwarsa, wanda hakan kan sanya gabban jikinsa su natsu, kuma hakan na yin tasiri kai tsaye wajen kwakkwafa ciwuka da ke da dangantaka da kwalwa ko zuciya, kuma masanan sun gwada hakan a lokuta da dama ga masu fama da rashin lafiya irin wannan, kuma sukan samu sauki a duk lokacin da suke sauraren karatun wadannan surori na alkur'ani mai tsarki.
366696