Bayan ta nakalto daga El Moudjahid ,Cibiyar kula da harkokin Alkur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: bincike kan hakkokin kasa da kasa da tushen kare hakkin dan adam suna daga cikin abubuwan da wannan taro yafi maida hankali a kansu kuma an fara kaddamarwa ne a jiya a cibiyar al'adu ta kasar Aljeriya kuma an samu halartar masana da masu bincike da ra'ayoyi kan hakkokin kasa da kasa inda suka gabatar da jawabobi kan haka tare da halartar Bu Abdallah Gulamullah ministan da ke kula da harkokin addinin musulunci a wannan kasa.
367829