Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labarai na (Ma'an) cewa; a wata zantawa da ta hada shi manema labarai yau a Gaza, Nafiz Azzam daya daga cikin jagoroin kungiyar Jihadul Islami, ya bayyana cewa Isra'ila tana wuce gona da iri a kan masallacin Quds, wanda kuma hakan nauyi na day a rataya kan musulmi da larabawa, da su dauki dukkanin matakan da za su iya wajen kawo karshen barazanar da masallacin Quds ke fuskanta daga daga Isra'ila.
A bangare guda kuma ya soki shiru da wasu bangarori na larabawa da musulmi ke yi kan tabargazar da Isra'ila take aikatawa a birnin Quds da ma sauran yankunan Palastinawa.
368983