Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran(SPA) cewa; daya daga cikin wadanda suka shirya gudanar da taron (Ahmad Saifi) shugaban kungiyar musulmin kasashen latin Amurka ya bayyana cewa; manufar gudanar da taron ita ce kara kusanto da fahimta tsakanin addinai, domin warware da dama daga cikin batutuwa da ake samun rashin fahimtar juna a kansu.
Taron dai ya samu halartar masana daga sassa daban daban na duniya, da suka hada masana kiristoci da musulmi, daga cikin kasashen musulmi da suka tura wakilansu har da kasashen Malazia, Indonesia, Masar, Plastine, Saudiyya, Syria, Mauritania da kuma Aljeria. Kuma mahalatar taron sun nuna gamsuwarsu da yadda ya gudana.
368916