IQNA

Fara Taron Kasa Da Kasa A Aljeriya Kan Mu'ijizar Alkur'ani Da Hadisai Ta Fuskar Ilimi

13:57 - February 25, 2009
Lambar Labari: 1748558
Bangaren kasa da kasa: A ranar Litinin ce aka bude taron kasa da kasa kan Mu'ijizar Alkur'ani da hadisan Manzo a birnin Alshlf da ke yammacin babban birnin kasar Aljeriya.
Cibiyar da ke kula da harkokin Alkur'ani a Iran Ikna ne bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Muhit ta watsa labarin cewa: wannan taro ya samu halartar mutane 300 da ya hada masu rajin kare hakkin dan adam ,manazarta day an jami'a na kasashen musulmi.a wajen wannan taro mahalarta taron za su yi bincike da bayani kan ayoyi da suka yi Magana kan fannoni daban-daban na ilimi kamar yanayin Dabi'a,yadda aka halicci dan adam,girgizar kasa, Masassarar rana da wata da kuma dangantakar rana da wata. Bayan sun yi bincike da nazari kan ayoyin alkur'ani har ila yau masu halartar taron suna dubi kan Hadisan manzon Allah da suma suka yi Magana da bayani kan ilimi a dukan bangarori.

368858

captcha