Cibiyar kula da harkokin Alkur'ani a Iran Ikna ce ta jiyo jaridar AlyaumAlelektrik ta Saudiya. Cewa wanan taro na kungiyoyin mahardata Alkur'ani tun ranar litin da ta gabata ce aka fara shi karkashin sa idon Muhammad bin Fahad Bin Abdul Aziz gwamnan yankin Sharkiya kuma an samu halartar shugabannin kungiyoyin mahardata Alkur'ani a wannan kasa ta Saudiya.Abdul rahman Muhammadu bin Al Rakib shugaban hadin guiwar kungiyoyin mahardata alkur'ani ya bayyana muhimmanci alfanon gudanar da irin wannan taro da cewa yin hakan zai taimaka masu harda da kokarin yin hardar a kullum da kuma fahimtar irin matsalolin da suke fuskanta.
368903