Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na ma'aikatar shari'ar Iran cewa; , bisa la'akari da cewa batun Palastinu da kuma halin al'ummar palastinu suke ciki musamman bayan kai hare-haren ta'addancin da Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta kai kan alummar Gaza, ya zama wajibi kungiyoyin lauyoyi da masu kare hakkin bil adama na kasashen musulmi su gudanar da zama, domin daukar matakan da suka dace wajen gurfanar da Haramtacciyar Kasar Isra'ila a gaban kotun manyan laifukan yaki ta duniya, bisa laifukan yakin da ta tafka kan fararen hula a Gaza.
Bayanin ya ce za a gudanar da zaman a mako mai kamawa.
369384