IQNA

Musulmin Kasar India Sun Nuna Fushinsu Kan Kona Takardun Alkur'ani

12:41 - February 28, 2009
Lambar Labari: 1749262
Bangaren kasa da kasa: Wasu mabiya addinin musulunci a kasar India sun nuna fushinsu dangane da kone takardun alkur'ani da wani mutum ya yi a lardin Braditch, wanda hakan ya jawo gudanar da zanga-zanga.
Kamfanin dillancin lbaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (albashir) cewa; tun bayan da musulmin lardin Bradtch na kasar Indiya suka samu labarin kone takardun alkura'ni da wani mutum mabiyin addinin Hindus ya yi, suka fio kan tituna domin nuna fushinsu kan wannan danyen aiki, inda suka bukaci mahukunta da su dauki matakan gaggawa wajen ladabtar da mutumin.
A nasa bangaren jami'an tsaron gwamnatin India sun sha alwashin Dakar matakan da suka dace dangane da lamarin, yanzu haka dai jami'an tsaron sun shiga neman mutumin ruwa a jallo, wanda shi kuma tuni ya buya.
Tuni mahukuntar kasa India suka sha alwashin shiga kafar wando daya da duk wanda ya nemi tayar da husuma ta hanyar tsokanar mabiya wani addini
369834
captcha