Cibiyar da ke kula da harkokin Alkur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga ofishin da ke kula da hulda ta kasa da kasa da karbar jama'a a majalisar shawara ta musulunci ta watsa rahoton cewa; ali Larjani shugaban wannan majalisa a wannan tattaunawa yayi nuni da yanayin da musulmi ke ciki musamman musulmin yankin gaza na wuce gonad a irin gwamnatin HKI na kai masu hare-hare ta sama da kasa da ruwa a tsawon kwanaki 22 ga kuma yadda aka killace su da hana kai masu duk wani taimako da agaji na abinci da magunguna da gyara masu muhalli. A wani bangare na tattaunawa ya yi nuna cewa wajibi ne musulmi su taimakawa yan uwansu na gaza. Shi ma shugaban kungiyar hadin kan malummai musulmi a duniya ya bayyana wajibcin musulmi su taimakawa yan uwansu musulmin Gaza daga zalumcin HKI .
369729