Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Nasij) cewa; bangaren da ke kula da bincike kan harkokin addinai na jami'ar azhar ya fitar da wani bayani a yau, dangane da cin zarafin da wani gidan talabijin Isra'ila ya yi wa annabawan Allah, dac hakan ya hada da manzon Allah Muhammad (SAW) da kuma Annabi Isa (AS) da mahaifiyarsa Maryam (SA).
Bayanin ya ci gaba da cewa; al'ummar musulmi ba za su taba amincewa da tozarta manzonsu da sauran annabawan Allah ba da gidan talabijin din Isra'ila ke yi, a kan haka ya zama wajibi kan gwamnatin yahudawan da ta daukin matakan gaggawa wajen taka wa irin wadanann shirye-shiryen na cin zarafin addinai birki.
370341