IQNA

Wulakanta Kur'ani Da Amurkawa Suka Yi Ya Fuskancin Fushin Afganawa

11:54 - March 01, 2009
Lambar Labari: 1749675
Bangaren kasa da kasa: Dubban musulmin kasar Afganistan sun fito kan tituna a sassa daban-daban na kasar domin nuna fushinsu kan wulakanta alkur'ani da sojin Amurka suka yi a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Almoslem) cewa; a ranar alhamis da ta gabata, sojojin mamayar Amurka sun kai wasu hare-hare a wasu yankunan fararen hular kasar Afganistan, inda suka kone wani masallaci, tare da kone alkur'anan da ke cikin masallacin, lamarin da ya jawo fushin miliyoyin al'ummar musulmi na wannan kasa, kafin kyaftawa da bisimilla aka fara gudanar da zanga-zanga a sassa daban daban na kasar, domin la'antar wannan mummunan aiki da sojin Amurka suka aikata.
A nasu bangaren jami'an tsaron gwamnatin kasar Afganistan ba su yi wata wata ba wajen afkawa kan masu zanga-zangar tare da tarwatsa su, inda suka yi amfani da kulake da barkonon tsohuwa wajen dakile zanga-zangar.

370170


captcha