IQNA

An Fara Gudanar Da Taron Kungiyoyi Masu Zaman Kansu Na Kasashen Musulmi A Morocco

10:12 - March 02, 2009
Lambar Labari: 1750286
Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da zaman taro na hadakar kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen musulmi a birnin Ribat na kasar Morocco.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (BNA) cewa; an fara gudanar da taron hadakar kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen musulmi a kasar Morocco, da nufin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi duniyar musulmi a yau, inda wakilai daga kasashe daban-daban suke halartar taron, da suka hada da kasashen Turkiya, Malazia, Syria, Kuwait, Bangaladesh, Masar da kuma mai masafkin baki Morocco.
Sakataren hadakar kungiyoyin masu zaman kansu a kasashen musulmi Najmi Sadiq Auglo, ya bayyana cewa zaman taron zai yi dubi a kan muhimman batutuwa da suka shafi kasashen musulmi, da hakan ya hada da batun talauci, jahilci da kuma matsaloli na zamantakewa. Ya kara da cewa taron kuma zai tabo batun Palastinu da halin da al'ummar yankin suke ciki.

370566


captcha