IQNA

Nan Ba da Jimawa Ba Za A Gudanar Da taron Kasa Da Kasa Kan Palasdinu Alamar Gwagwarmaya,Gaza layar Ta'addanci

10:40 - March 02, 2009
Lambar Labari: 1750409
Bangaren kasa da kasa: Mamba a komitin zartarwa na majalisar Shawara a Iran ya bada labarin gudanar da taron kasa da kasa kan Palasdinu alamar gwagwarmaya ita kuwa gaza layar Yan ta'adda da majalisar shawara ta shirya a ranekun laraba da Alhamis masu zuwa.
Malam Muhammad Rida Mirtaj shugaban komitin hulda da palasdinu da Labanon a majalisar shawarar musulunci a iran a wata hira da cibiyar da ke kula da harkokin alkur'ani a Iran Ikna ya bayyana cewa: a wannan taro za a samu halartar shugabanni day an majalisar dokoki daga kasashe talatin na kasashen musulmi da larabawa kuma hatta wakilai daga kasashe dab a na musulmi ba za a samu halartar wakilansu a wannan taro. Kuam ya kara da cewa a lokacin bude wannan taro za a samu halartar bangarori uku na kasar masu karfi fada a ji wato shugaban kasa da gwamnatinsa,Majalisar shawara ta kasar Iran da kuma bangaren kotun kolin kasar saboda muhimmancin wannan taro na taimakaw al'ummar palasdinu da kalubalantar ta'addancin HKi kan al'ummar Palasdinu a yankin Gaza.

371055

captcha