Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (alhayat) ta kasar Saudiyya cewa; A wani bayani da sakataren cibiyar hukunce-hukuncen musulunci ya fitar, yabayyana cewa tozarta matsayi manzon Allah da tashar talabijin Isra'ila ta yi a cikin wani shirinta, ba shi ne karo na farko day a hudawan sahyuniya suka yi hakan ba, domin kuwa wannan aiki ne da tarihi ya tabbatar musu da shi, inda suka shahara da tozarta annabawan Allah. Bayanin ya ce taba manzon Allah (SAW) taba addinin musulunci ne da musulmi baki daya.
Bayanin ya yi kakkausar suka kan wannan wannan mummunan aiki na tasahar talabijin din Isra'ila, kamar yadda bayanin ya yi Alladawai da wani shiri makamancin haka da tashar ta watsa, wanda ya ci zarafin annabi Isa (AS) da Maryam (SA) mahaifiyarsa.
371566