IQNA

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Na Neman Daukaka Ne Ga Duniya Musulmi

16:25 - March 05, 2009
Lambar Labari: 1752093
Bangaren siyasa da zamantakewa: Shugaban bangaren da ke kula da bincke-binciken ilimi a Iran ya bayyana cewa; har kullum Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana neman daukakar kasashen musulmi ne.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; shugaban bangaren da ke kula da gudanar da bincike-binciken ilimi a kasar Iran (Mostafa Poor Mohamamdi) a wani bayani day a gabatar a wajen wani taro a lardin Sistan da Balochestan ya bayyana cewa; jamhuriyar musulunci ta Iran tana neman daukaka ne ga duniyar musulmi a kowane lokaci ba tare da la'akari da banbancin fahimta ta mazhaba ba, domin kuwa musulunci shi ne ya hada al'ummar musulmi ba mazhaba ba.
Ya ci gaba da cewa; Iran ta taimaka ma al'ummar Afganistan tsawon lokaci, kuma ta karbe su a lokacin da suke bukatar mafaka tare da bas u dukkanin abin da suke bukata. Hakan nan Iran ta kwashe tsawon shekaru tana taimaka ma al'ummar Palastinu da ke karkashin danniya da zaluncin yahudawan sahyuniya, daga ciki kuwa hard a taimakon da Iran din take baiwa al'ummar gaza a halin yanzu.

373105

captcha