IQNA

Aya Ta 7 A Cikin Surat (Ra'ad) Tana Umurtar Manzo (SAW) Da Yin wa'azi

10:53 - March 07, 2009
Lambar Labari: 1752574
Bangaren fikira: Aya ta 7 a cikin surat ra'ad tana umurtar manzon (SAW) da ya yi wa'azi ga daidaikun mutane da kuma al'umma baki daya.
A wata zantawa da kamfanin dillancin labaran Ikna ya gudanar tare da wakilin jagoran juyin juya halin musulunci a Iran a jami'ar azad reshen lardin Azarbaijan da ke gabacin Hojjatol islam (Mansur Barati) ya bayyana cewa; manzon Allah ya zo da sako ne ga dukkanin talikai, inda Allah ya fara umurtarsa day a yi wa'azi da tunatarwa ga mutane daidaiku da kuma al'umma baki daya, wanda hakan ke nuni da cewa sakon da manzon Allah ya zo da shi daga ubangijinsa sako ne na dukkanin dan adam, ba sako ne na wasu kebantattun mutane ba.
Ya ce dole ne ayi koyi da abin da shi kuma ya aikata shi a aikace matukar dai ana son samun kubuta daga fushin ubangiji, ya kara da cewa; malamai sun e nauyi ya rataya kansu wajen ci gaba da isar da wannan sako mai tsarki domin shiryar da al'umma.


373473
captcha