IQNA

An Shirya Gasar Al'adun Musulunci Tsakanin Matasa Masu Kishin Addini A Baku

15:10 - March 07, 2009
Lambar Labari: 1752818
Bangaren Al'adu; a wannan lokaci na tunawa da ranar haifuwar fiyayyen halitta (SWA) a shirya olumpiyar Addini Da tunani a babban masallacin Baku babban birnin kasar Azarbaijan.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa:wannan gasar an bata sunan Olumpiyar tunawa da ranar haihuwar fiyayyan halitta inda matasa za su nuna kwarewa da yadda za su taimaka wajen yada addini.Masu son mahalarta wannan gasa suna iya aiko da bukatarsu ta hanyar Emil ko kuma su gabatar da kansu ta hanyar adreshin shafin wannan gasa. Kuma lokacin rufe rubuta sunayen wannan gasa har zuwa ranar 13 ga watan maris din wannan shekara ta 2009 kuma gasa ta hada tarihin Alkur'ani da al'adun musulunci da lamurra da suka shafi siyasa da zamantakewa.

373645
captcha