IQNA

An Bayyana Iran A Matsayin Kasar Da Ke Kare Hakkokin Palastinawa

16:59 - March 08, 2009
Lambar Labari: 1753097
Bangare siyasa: A cikin shekaru 30 da suka gabata, Iran ce kasar da aka sani a duniya tana kare hakkokin Palastinawa bil hakki da gaskiya a duniya fiye da sauran kasashe.
A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da shugaban kwamitin kula da harkokin Labanan da Palstinu a majalisar shawara ta Iran Mohammad Reza Mir Tajuddin, ya bayyana cewa Iran ce kasar da ta fi kowace kasa a duniya shiga gaba wajen kare hakkokin al'ummar palastinu, ya ce tun bayan samun nasarar juiyin juya halin musulunci a Iran, sha'anin Palastinu ya zama daya daga cikin muhimman batutuwa da Iran take mayar da hankali kansu, inda take kare hakkokinsu a matsayi na kasa da kasa, da kuma bas u taimako na karfin gwiwa da ma abubuwan bukata na rayuwa, domin rage damur da suke ciki sakamakon cin zalun da danniyar da suke fuskanta tsawon shekaru daga yahudawan sahyuniya.
Ya ce Iran ba za ta gushe tana bayar da irin wannan taimako da goyon bayan al'ummar Palastinu ba har lokacin da za su fice daga kangin danniyar yahudawan sahyuniya.

373478
captcha