IQNA

Yakin Gaza Ya Tona Asirin Yammacin Turai Da Masu Daure Wa Isra'ila Gindi

16:56 - March 08, 2009
Lambar Labari: 1753099
Bangaren siyasa: Sakataren majalisar tsaron kasa a Iran ya bayyana cewa yakin Gaza ya tona asirin kasashen yammacin turai da kuma masu goyon bayan Isra'ila ido rufe, wajen aikata zalunci da danniya kan al'ummar Palastinu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga sakataren majalisar tsaron kasa a Iran Sa'id Jalili cewa; yakin da Isra'ila ta kaddamar kan al'ummar Gaza inda ta kashe fararen hula da dama, da suka hada da daruruwan kananan yara da mata, hakan ya tona asirin yammacin turai, wadanda su ne kan gaba wajen mara wa gwamnatin yahudawan sahyuniya baya a dukkanin ayyukan ta'addancin da take aikatawa kan al'ummar Palastinu da ma na yankin baki daya, gami da wasu munafukan kasashe a yankin da suke goyon bayan Isra'ila a boye na tsawon lokaci ba tare da an Ankara ba, amma yakin Gaza ya bayyana masu goyon bayan al'ummar Palastinu da sha'aninsu na gaskiya, da kuma masu munafuntar al'ummar Palastinu, kama daga kasashen yammacin turai har zuwa mufukan kasashen musulmi da na larabawa.

373955






captcha